Rikici Ya Kunno Kai Kan Zaben Abokin Takarar Atiku Abubakar - Leaders Hints

Admin
1

Rikici Ya Kunno Kai Kan Zaben Abokin Takarar Atiku

Alhaji Atiku Abubakar 
Dan Takaran Sugaban Kasa a Jamiyyar PDP
2023


Kamar yadda Gidan Jaridar Aminiya ta ruwaito, Sabon rikici ya kunno kai a kan zabin dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, a yayin da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, Atiku Abubakar ke kara tuntubar masu ruwa da tsaki.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike na barazanar ficewa daga PDP, muddin Atiku ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Wike ya yi barazanar ce a bayan an gabatar da sunan Okowa a matsayin daya daga cikin mutanen da ake so su yi takara tare da Atiku, a lokacin taron gwamnonin jam’iyyar da Atiku kan zabin dan takarar da zai mara wa Atiku baya.

A ci gaba da tuntubar da Atiku Abubakar ke yi, zai gana da tsofaffin gwamnoni da ministocin jam’iyyar a karshen makon nan a Abuja.

Ko a ranar Laraba, dan takarar ya yi irin wannan zama da gwamnonin PDP.

Wata majiya mai kusanci da zaman da za a yi a karshen mako ta ce hakan na daga cikin kokarin dan takarar na “daidaita bukatun dukkan bangarorin jam’iyyar kafin ya kai ga zabo mataimakin nasa.”

Majiyar ta ce a taronsa da gwamnonin sun nemi ya zabi daya daga cikinsu, ciki har da Nyesom Aike na Jihar Ribas, Nyesom Aike, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jami’yyar.

Sauran su ne Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa; Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel; da Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri.

Majiyar ta ce: “Dan takarar mutum ne mai kaifin hankali kuma zai so mutumin da PDP za ta iya lashe zabe da shi.

“Dole ne ya yi tunanin mutumin da ya fahimci yanayin tattalin arziki na zamani saboda mummunan halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, tare da daidaita muradun yanki da siyasa. Mun kuma san cewa ba lokaci yana neman kurewa.”

Kakakin Atiku, Mazi Paul Ibe, ya tabbatar da shirin dan takarar na ganawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

"Haka ne, ana ci gaba da tuntubar juna kuma [Atiku] ya shirya tarurruka da dama a karshen mako, tare da tuntubar jam’iyyar domin gabatar da abokin takara da ’yan Nijeriya za su so su kada musu kuri’a su ci zabe.”

Rikicin ya kunno kai


A yayin da Atiku Abubakar ke ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyyar kan abokin takarar tasa, alamu na nuna cewa idan ba a yi abin ya kamata ba, jam’iyyar na iya fadawa cikin wani rikici.

Wata majiya da ta halarci wani zama da Atiku ya kira ta ce Gwamna Wike ya yi barazanar cewa idan aka dauki Gwamna Okowa na Jihar Delta a matsayin abokin takarar Atiku, to shi zai fice daga PDP.

Majiyar ta ce tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori, yana daga cikin shugabannin jam’iyyar da suke adawa da zabin Gwamna Ifeanyi Okowaa matsayin abokin takarar Atiku.

Akwai kuma mutanen da aka ce suna Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP ke so dan takarar ya dauki abokin takararsa daga cikinsu.

Mutanen sun hada da tsohuwar Ministar Kudi kuma Darakta-Janar ta Kungiyar Ciniki ta Duniya (WTO), Dokta Ngozi Okonjo-Iweala; da tsohon Shugaban Riko na Majalisar Wakilai, Emeka Ihedioha; da kuma tsohon Gwamnan Jihar Delta, Emmanuel Uduaghan.

Post a Comment

1Comments
Post a Comment
Your Responsive Ads code (Google Ads)

#buttons=(Accept !) #days=(20)

Welcome To Leaders Hints! Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !