Hudan Noma (Tractor) kyauta a Mazabar Darazo/Ganjuwa - Mansur Manu Soro

Admin
3

 

Hon Mansur Manu Soro
Ganjuwa/Darazau

Hudan noma (Tractor) kyauta a mazabar Darazo/Ganjuwa 

A karshen shekarar 2021 na samu daman samar da tractor, taki buhu 2,500, famfon bayi 500, fanfon feshi 500 da injin girbin shinkafa 22 wa manoman mu inda muka yi organizing din su suka kafa kungiyar Darazo-Ganjuwa Farm Mechanization Support Initiative (DAGFAMSI) suka yi rajista da FGN.

Wannan kungiyar manoma tazo da tsari na hadin gwuiwa tsakanin ta da FG ta offishina da kuma BASG ta hannun BSADP.

Ina mai farin cikin sanar da manoman mu cewa wannan kungiya ta fara amfani da wannan tractor a gonakin dake mazabar Darazo/Ganjuwa bayan samun ruwan sama da akayi a kwanakin nan. 

Manoman mu a Darazo da Ganjuwa dake bukatan services na hudan gonakin su zasu iya tuntubar kodinetoti na kungiyar DAGFAMSI dake gundumomin su (a duba sunayen su da lamban wayoyin su a kasa). 

Manufan mu a bangaren noma shine samar da yanayi da zai bada sauki wa manoman mu ta hanyar amfani da mashuna, irin shuka da takin zamani. Yanayi da zai rage wahala da ake sha wajen yin noma ya kuma habaka amfani da ake samu. 


Mun dukufa wajen ganin mun kara yawan tractocin a wannan mazaba ta hannun kungiyar DAGFAMSI da kuma samar da tsari da zai wanzar da wannan shiri (sustainability) Insha Allahu.

Rep. MMS 

MHR 

10/06/22

Post a Comment

3Comments
Post a Comment
Your Responsive Ads code (Google Ads)

#buttons=(Accept !) #days=(20)

Welcome To Leaders Hints! Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !